Gasar rubutun makala ta Bakadamiya Encyclopaedia za ta kasance wata babbar dama ce ga masu bibiyan wannan taska – dalibai, marubuta, ‘yan jarida da masu nazari da bincike musamman a harshen Hausa – domin su inganta bincikensu, su faɗaɗa tunaninsu, kuma su samar da ingantattun bayanai masu amfani a fannoni daban-daban na rayuwar dan adam.
Manufofin gasar
- Janyo hankalin jama’a wajen ƙara ƙaimi a karatu, bincike da kuma rubutu mai inganci da ma’ana
- Haɓaka ƙwarewar masu sha’awar karatu, bincike da rubutu a fannoni rayuwa daban-daban cikin harshen Hausa
- Samar da muhimman bincike da rubutu a fannonin kimiyya cikin harshen Hausa
- Inganta tsarin bincike da jero bayanai na Encyclopaedia ta hanyar samar da sababbin rubuce-rubuce na ilimi.
- Samar da tarin ilimi na dindindin a Bakandamiya Encyclopaedia
Ɓangarorin da gasar za ta mayar da hankali
Wannan gasa za ta riƙa gudana a duk ƙarshen wata, tare da batutuwa ko matsalolin bincike da za a bayar domin a yi rubutu mai tsari da ilimantarwa. Fannoni da batutuwan gasar za su kasance kamar haka:
- Kimiyya (Physics, Chemistry, Biology, Mathematics)
- Fasaha (Technology)
- Lafiya (Health & Medicine)
- Tarihi (History)
- Literature (Adabi)
- Ilimin zamantakewa (Social Science)
- Sauran fannoni na ilimi
Yadda gasar za ta gudana
- Kowace ranar 10 ga wata za a zo da muhimmiyar tambaya da ta shafi maudu’an da aka ambata a sama. Kuma tambayar za a dora ta ne a shafin Facebook na Bakandamiya Encyclopaedia.
- Tambayar za ta buƙaci cikakken bayani irin na rubutun encyclopedia (wato conceptual analysis) da bai yi ƙasa da kalmomi 1500 ba.
- Za a ba wa mahalarta gasar awa 120 (kwanaki 5) daga lokacin da aka dora tambayar don su dora amsarsu ko rubutunsu.
- Masu ba da amsa za su dora shi ne ta hanyar wallafawa a ƙarƙashin posting ɗin tambayar da aka yi, wato a matsayin reply na wannan tambayar.
- Kwamitin alƙalai za su yi nazari bisa ka’idoji su tantance sannan su fitar da rubutu guda ɗaya mafi inganci.
- Za a sanar da sakamako a ranar 1–10 na kowane sabon wata.
Abubuwan da kwamitin alkalai za su duba
- Gamsassun bayanai da misalai – maki 25
- Tsarin bayanai da nuna sahihancin bincike – maki 25
- Ka’idoji, salo da tsarin rubutu – maki 20
- Kawo muhimman manazarta (references) – maki 10
- Cikan kalmomi (1500 – 2000) da dacewar bayanai – maki 10
- Dora cikakken amsa a kan lokaci – maki 10
Sauran sharuɗɗa da ƙa’idojin gasar
Ga wasa sauran sharuɗɗa da ka’idoji da za a lura da su don shiga gasar:
- Mutum biyu ba za su iya shiga gasar a lokaci guda ba.
- Ba za a yi amfani da rubutun AI ba.
- Ma’aikatan Bakandamiya ba za su iya shiga gasar ba.
Kyaututtuka
Akwai awalaja da kyaututtuka ga wanda ya yi nasara kamar haka:
- Kautar kuɗi N10,000
- Za a ba shi/ta certificate
- Za a buga makalarsa/ta da sunansa/ta a Bakandamiya Encyclopaedia
- Za a lissafo sunnansa/ta a wuri na musamman a website na kamfanin Bakandamiya.
Kammalawa
Wannan gasa ta wata-wata za ta ba da gudummawa mai girma wajen cike giɓin ilimi da bincike a harshen Hausa, tare da samar da wata kafa ta ƙarfafa wa matasa ɗabi’ar yin karatu, bincike da rubutu a fannonin rayuwa daban-daban. Muna fatan wannan yunkuri zai samu karɓuwa domin ya zama ginshiƙin ɗaukakawa da bunƙasa ilimi a tsakanin al’umma.
