Hikaya Monthly Quiz yanzu ta koma Hikaya Monthly Challenge. Kana, kuna iya samun kudi har N10,000 da wasu kyautukan idan kuka yi nasara.
Hukumar gudanarwa ta Bakandamiya na farincikin sanar da ɗaukacin marubuta, masu karatu, mabiya, da ma dukkan masoya Bakandamiya Hikaya cewa, a sabuwar shekarar da za mu shiga ta 2026, akwai wani gagarumin albishir game da gasar da take sakawa a kowace wata, wato Hikaya Monthly Quiz.
Kamar yadda ku ka sani, awalajar gasar naira ₦5000. To amma yanzu baya ga awalajar, liyafa ta ci gaba sobada akwai abubuwa da dama da aka sabunta game da gasar kamar haka:
1. Awalajar ta koma naira ₦10,000 daga ₦5000.
2. Duk amsar da ta yi nasara za a buga ta da sunan marubucin a Hikaya blog.
3. Duk wanda ya yi nasara zai samu subscription na wata guda da zai more karatu a manhajar Hikaya.
4. Za a saka sunan duk waɗanda suka yi nasara a wani sashe na musamman a shafin kamfanin Bakandamiya.
5. An canza wa gasar suna daga Hikaya Monthly Quiz zuwa Hikaya Monthly Challenge
6. Tambayoyin gasar na iya zuwa a harshen Hausa ko Turanci, don haka a harshen da tambayar ta zo, a shi za a bayar da amsa.
7. Ma’aikatan Bakandamiya ba za su iya shiga gasar ba.
8. Ba a yarda mutane biyu ko fiye da haka su shiga gasar da suna ɗaya ba.
9. Ba a yarda a yi amfani da AI wajen amsa tambayoyin ba.
10. Awa 72 (kwana uku) masu shiga gasar ke da shi kafin a rufe.
Abubuwan da ake dubawa domin zaɓar zakara a gasar
- Wanda ya fi bayar da gamsassun bayanai da hujjojin da suka dace – maki 25
- Wanda ya fi fayyace bayanai da suka nuna sahihancin bincike – maki 25
- Wanda ya fi kiyaye ƙa’idoji da salon rubutu mai tsari – maki 20
- Wanda ya fi kawo manazarta da suka dace a cikin da karshen makala – maki 10
- Wanda ya kawo cikakken makala da bai gaza kalmomi 1500 zuwa 2000 – maki 10
- Wanda ya fara amsa tambayar daidai – maki 10
Za a fara amfani da wannan sabon tsari ne daga ranar 5 ga watan Janairu 2026.
Fatan alheri ga dukkan masu sha’awar wannan gasa.
The Bakandamiya Team
