Idan kai marubuci ne ko marubuciya, Bakandamiya ta zo da wani sabon tsari na musamman don ba ku damar buga rubutunku su kai ko’ina a amfana da su sannan kuma ku samu yan kudi da zai taimaka muku wajen cigaba da ayyukanku na ilmantarwa, fadakarwa da nishadantarwa.
Bangarorin rubutu
Wannan sabon tsari zai baiwa marubuta dama a bangarorin rubutu guda uku:
Kagaggun labarai (Hausa novels)
Marubutan kagaggun labarai, wato Hausa novels, za su iya samun N2000 don buga kowane shafi guda na labarinsu a taskar Bakandamiya. Ku latsa nan don ganin misalin wannan rubutu da ya cika ka’ida.
Marubuta makala (Article)
Masu rubutun makala ta musamman a fannoni rayuwa daban-daban za su iya samun N3000 ga kowace cikakkiyar makala da su ka buga. Fannonin sun hada da kiwon lafiya, kimiyya da fasaha, tarihi, zamantakewa, kasuwanci, adabi da makamantansu. Ku latsa nan don ganin misalin rubutun makala da ya cika ka’ida.
Girke-girke
Masu koyar da girke-girke na iya yin rubutu da zai koyar da a kalla girki daya, sannan za su iya samun N1000. Ku latsa nan don ganin irin tsarin rubutun girke-girke da ya dace.
Muhimman ka’idoji
1. Assasa rubutu
Wajibi ne rubutun da marubuci zai buga don shiga wannan tsari na biyan kudi ya zama rubutunsa ne da ya ke da hakkin mallaka akai. Duk lokacin da Bakandamiya ta gane sabanin hakan ta na da hakkin datakar da marubuci a wannan tsari.
2. Sabontan rubutu
Wajibi ne ya zamanto rubutun da marubuci zai shiga wannan tsari da shi ya kasance sabon rubutu ne ba a sanya shi ko buga shi a wata kaf aba gabannin sanya shi a Bakandamiya. Babu laifi bayan kammala buga duk shafukan littafin kuma ya cika duk ka’idoji na Bakandamiya a sanya shi a wata kafar na daban. A duk lokacin da Bakandamiya ta gane sabanin hakan ta na da hakkin datakar da marubuci a wannan tsari.
3. Ingancin rubutu
Bakandamiya za ta duba ingancin rubutu ta muhimman bangarori guda uku:
- Muhimmanci da isar da sakon rubutu
- Bin ka’idojin rubutu
- Tsarawa da bugawa mai kyau, wato formatting
4. Views, Likes, Comments
A duk lokacin da marubuci ya buga rubutunsa na farko, sannan aka amince da shi, wato bayan ya cika dukkan ka’idoji na rubutu da kuma akalla LIKES 20, da COMMENTS 10 da kuma VIEWS 1000 (na girke-girke VIEWS 500 ya wadatar), to zai iya buga rubutunsa na gaba (shafi na gaba).
5. Yawan kalmomi
- Kagaggun labarai (Hausa novels) – 2500
- Makalu – 1500
- Girke-girke – 300
Marubuci na iya wuce adadin kalmomin da aka bayyana a sama matukatar yana da bukatar yin hakan. Abin so dai kada su gaza adadin.
6. Amfani da hotuna
Yana cikin ka’ida marubuciyar girke-girke ta yi amfani da hoto, a kalla biyu zuwa uku, wajen nuna matakan girke-girkenta.
Sanya hoto a tsakiyar makala (article) yana da muhimmanci wajen isar da sako idan akwai bukatar yin hakan, amma bai zama dole ba idan babu bukata.
Wajibi ne duk hoton da marubuci zai yi amfani da shi ya kasance yana da hakkin mallakar hoton ko kuwa ya zamanto ya rubuta sunan mamallakin hoton a kasa don bin ka’ida.
7. Hanyar buga rubutu
Da farko marubuci zai yi rajista a taskar Bakandamiya (idan da bai yi ba kenan), sannan sai ya tafi sashen makala ya buga rubutunsa. Marubuci ya tabbatar cewa rubutunsa sun inganta sannan ya bi ka’idojin buga rubutu, wato formatting, kamar yadda ya kamata. Yin amfani da computer zai fi taimakawa gaya wajen buga tsabtataccen rubutu mai kyau.
Bayan marubuci ya buga rubutunsa sai ya kwafi link na rubutun ya turowa Bakandamiya ta email: admin@bakandamiya.com
8. Hanyoyin tantance rubutu
Idan rubutu ya cika dukkan ka’idoji to marubuci zai samu amsar sakon amincewa ko rashin amincewa ta hanyar email da ya aiko sakonsa da farko.
Idan rubutu ya yi baya sosai wajen cika ka’idoji, to kai tsaye daga bugun farko Bakandamiya za ta aikowa marubuci da amsar rashin amincewa.
Idan kuma bai cika ka’idoji ba, to amma ya kusa cikawa, Bakandamiya za ta hada shi da wasu daga cikin ma’aikatanta wadanda za su taimakawa marubucin don ya cika wadannan ka’idojin. Za su yi aiki da shi kama daga buga rubutu na farko har zuwa kamar na uku ta yadda za su tabbatar ya cika ka’idar. Idan hakan bai yiwuwa ba sai su dakata daga bugu na uku.
Wadanda suka cika ka’idoji za su cigaba da buga rubutunsu, idan ya kai adadin biyan kudi su nema a turo musu, sannan Bakandamiya za ta ci gaba da bibiyar rubutun nasu don ganin cewa kullum an samu cigaba.
9. Biyan kudi
Marubuci zai iya neman kudinsa ne bayan ya buga a kalla amintattun rubutu guda 5 (misali in ya buga shafukan labari guda 5, zai nemi N10,000; haka N15,000 na makalu 5; sannan N5000 na rubutun girke-girke guda 5. A duk lokacin da marubuci ya bukaci kudinsa, zai iya samu ne a karshen watan da ya aiko da bukatar tasa, kuma za a tura masa ne ta hanyar asusun bankinsa da ya aikowa Bakandamiya.
10. Ka’idoji da suka shafi hakkin mallaka
Duk marubucin da ya buga rubutunsa yana da hakkin mallakar rubutun nasa gwargwadon yadda Bakandamiya ta ke da shi. Har abada rubutunsa ne kuma da sunansa za a yada rubutun; ba za a saka sunan wani a rubutun a madadinsa ba.
Marubuci bai da ikon sauke (wato deleting) wannan rubutun sai tare da amincewar Bakandamiya, amma zai iya gyara (wato editing) don kara inganta rubutun. Bakandamiya na da ikon buga rubutun a wasu taskokinta na daban tare da sunan marubucin don yadawa da amfanin al’umma.
A kowane lokaci Bakandamiya na da ikon gyara ga duk ka’idojin da aka zayyana a sama gwargwadon juyawar al’amura, to amma duk sabon gyara ko tsari da aka zo da shi zai shafi ayyukan da za su zo a gaba ne, ba wadanda suka gabata ba.
Duk mai bukatar karin bayani na iya tuntubarmu kai tsaye a taskar Bakndamiya, ko kuwa ya rubuto mana email ta adireshin email namu da muka bayar a can sama, ko kuwa ta WhatsApp a +234 (0) 9072304845.
Kuna karanta wannan bayanai da ka’idoji ne a shafin business na Bakandamiya. Don zuwa taskar Bakandamiyar kai tsaye ku yi rajista sai ku latsa nan.
Sai mun ji daga gareku.
Tabbas wannan wata huɓɓasa ce da za ta farfaɗo da ruhin Adabi!
Madallah da Bakandamiya!
Godiya muke!
Masha Allah
Gaskiya kuna matukar kokari sosai wajen kai harshen Hausa kololuwa, kuma muna alfahari da wannan jajircewa da kuke Allah ya shige maku gaba.
Amin Ya Rabb. Allah Ya bar zumunci.
Fulairahabibudubanni@gmail.com
Gaskiya tsarin ya yi kyau Allah ya bamu ikon yi, ya taimaka mana baki dayan mu.
Amin Ya Rabb. Mun gode
Allah ya tabbatar da Alkhairee.
Amin Ya Rabb. Godiya muke.
Allah ya taimaka
Allahumma amin. Mun gode.
Masha Allah, hak’ik’a abu ya yi ma’ana. Allah ya yi mana jagora na alkhairi, amin.
Amin Ya Rabb. Godiya muke!
Allah ya taimaka. Wannan tsarin yayi kyau sosai zai farfaɗo da adabi da cigabansa.
Allahumma amin. Muna godiya.
Da kyau
Allah ya karo Fahimta
Amin. Mun gode!
Assalamu alaikum alaikum jama’a gaskiya wannan tsarin yana da kyau kuma zai taimaka kwarai ga wadanda basu da sana’a samun aikin yi da kuma kara farfaɗo da kwararrun marubuta masu hazaka a arewacin najeriya da fatar ALLAH ya taimaka fatan alkhairi bakan damiya
Allah Ya sa hakan! Muna godiya da wannan karfafa guiwa.
Muna murna tare da farin ciki da wannan cigaba da kuka zo muna dashi
Muna godiya! Allah Ya bar zumunci.
Masha Allah! Haƙiƙa wannan tsari ne mai kyau, wanda kuma zai ba wa mutane masu fiƙira da sha’awar rubuce-rubuce damar amfana da baiwar da Allah Ya hore musu. Ba zamu bari a barmu a baya ba.
Godiya muke. Allah Ya bar zumunci.
Madallah da wannan yunƙuri. Haƙiƙa wannan sabon tunani a cikin rubutun Hausa da ya kamata a ƙarfafe shi.
Muna godiya kwarai da karfafa guiwa. Allah Ya bar zumunci.
sai mun zo
To madallah, sai mun gan ku.
Madalla
Yauwa, muna godiya!