Skip to content

Bakandamiya ta shirya bita akan tsari da salon rubutun labari

Share
Bitar rubutun labari

Ina masu sha’awar rubutun Hausa novels ko shiga gasar rubuce-rubuce, har ma da masu sha’awar karance-karance? Bakandamiya ta shirya muku bita ta musamman akan tsari da salon rubutun gajeren labari, wanda shahararren marubucin nan na littafin TEKUN LABARAI, wato Danladi Z. Haruna, zai gabatar.

An shirya wannan bita ne don samun damar yin munakasha da karar juna tsakanin marubuta da ‘yan ‘uwansu marubuta da kuma masu sha’awar karance-karance.

Bitar wacce aka yi wa taken TSARI DA SALON RUBUTUN SHIGA GASAR GAJEREN LABARI za ta tabo maudu’ai guda shida.

Maudu’an bita

  1. Waiwaye akan ka’idojin rubutu
  2. Ka’idojin gajeren labari
  3. Matakan kirkirar labari – Five fingertips
  4. Dabarun budewa da rufewa
  5. Matakan rubuta gajeren labari
  6. Misalan gajerun labarai

Bitar za ta kasance ne a taskar Bakandamiya, wato mutum na bukatar ya yi rajista a Bakandamiya sannan ya shiga group din MARUBUTA wanda a can ne za a gudanar da bitar. Ga tsarin nan daki-daki yadda zai kasance.

Tsarin halartar bita

  1. Da farko mutum zai sauke manhajar Bakandamiya a wayarsa sannan ya yi rajista (idan har bai rigaya ya yi ba kenan). Don sauke manhajar sai a latsa nan. Sannan don ganin bayanin yadda ake yin rajista shi kuma sai a latsa nan.
  2. Da zarar mutum ya yi rajista, sai ya nemi zauren, wato group din MARUBUTA. Za a iya binciko shi da sunansa ko kuma a je sashen zauruka a neme shi. Har ila yau, ana iya latsa nan don ganin bidiyon yadda ake shiga, wato joining na zaure.
  3. Abu na uku sai mutum ya jira ranar da za a yi bitar, kuma a daidai lokacin da aka sanya, sannan ya shiga wannan zauren don halartar bitar.

Ranaku da lokatan bita

  • Ranar Bita: 15 – 20 June, 2020 (wato kwanaki biyar za a yi na bitar)
  • Lokacin Bita: 8:00 pm (kowane rana, agogon Nigeria da Niger)
  • Wurin Yin Bita: Taskar Bakandamiya, cikin zauren MARUBUTA

Karin bayani

Mai gabatar da bitar, Malam Danladi Haruna, zai yi amfani da rubutu da sauti da hotuna har ma da bidiyo wajen isar da sakonsa, sannan masu halarta za su tattauna tare da yin tambayoyi.

A kowane karshen bita, mai gabatar da bitar zai bada aiki da za a yi a kawo gobe. In Allah Ya so bita ce da bayan kammalawa duk mutumin da ya halatta zai fahimci wani abu da zai amfane shi/ta, walau daga wurin malami mai bita ko kuwa abokan halartar bitar.

Daga karshe, duk wanda ya halacci wannan bita sannan ya cika ka’idojin halattar, zai samu shedar halatta, wato certificate. Ranar fara bita za a yi cikakken bayanin ka’idojin.

Duk wanda yake da tambaya ko neman karin bayani zai iya tuntubar: 0803744258, 08030764060

Allah Ya yi mana jagora kuma Ya sa mu amfana da abin da za mu koya.

4 thoughts on “Bakandamiya ta shirya bita akan tsari da salon rubutun labari”

    1. Dalhatu Abubakar, za a baiwa duk wanda ya halacci wannan bita shedar halatta, wato certificate. Amma akwai ka’idoji da mai halatta zai cika kafin ya samu wannan sheda, misali zai kasance ya halacci akalla kashi 60 na darussan, kuma ya gudanar da duk ayyukan da malamin bita ya bayar akalla shima kashi 60. In sha Allahu ranar fara bita, za a yi cikakken bayanin duk wadannan ka’idoji. Mun gode.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

×