Skip to content

Gagarumin gasar muhawara don kungiyoyin marubuta

Gasar muhawara 1

Taskar Bakandamiya ta shirya gasar muhawara na musamman don kungiyoyin marubuta.

Jigon Muhawara

Koyar da Dabarun Rubuce-Rubuce ta Hanyar Kafar Sadarwa (Internet)

Sannan don ƙara zaƙulo haziƙan marubuta.

Ranar Farawa

Insha Allahu za a fara wannan gasa ranar 24/11/2020.

Ranar Kammalawa

Kuma insha Allahu za a kammala wannan gasa ranar 2/2/2021.

Kyautuka da Za a Bayar

1) Duk ƙungiyar da tayi ta farko tana da kyautar  kambun girmamawa na musamman ga mi da kyautar manyan litattafai na adabi tare da kudi naira dubu hamsin (N50,000)

2) Ƙungiyar da tayi ta biyu itama akwai kambun girmamawa na musamman tare kuma manyan littattafan adabi, da kuma kyautar kudi naira dubu talatin (N30,000)

3) Ƙungiyar da tayi da uku kuma zata samu kyautar kambun girmamawa na musamman tare da manyan littattafan adabi,da kuma kyautar kuɗi naira dubu ashirin (N20,000)

4) Kowacce ƙungiya da ta halarci wannan gasa akwai kyautar katin shaida wanda zai nuna cewa sun halarci wannan gasa.

5) Za a bayar da wannan kyautuka ne a birnin Kano ta dabo ci gari mai mata mai mota mai Dala da Gwauron Dutse garin Dan Abdu giwar sarki, inda za ayi gangamin gayyatar manyan marubuta,sarakuna da yan kasuwar littafi dama sauran  manyan baƙi na musamman, kowacce ƙungiya za su so don ƙarɓar kyautar da suka samu,wannan taro zai gudana ne da zarar an kammala gasar,sanarwa  ranar taron da kuma lokacin taron  duk za ta zo daga baya.

Ana iya latsa nan don karanta cikakken ka’idojin muhawarar.

Share

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

×