A ranakun 15 zuwa 20 ga watan Yuni na wannan shekara ta 2020 ne aka gabatar da bitar da Bakandamiya ta shiryawa marubuta da makaranta wadda Malam Danladi Z. Haruna ya jagoranta, kamar yadda aka sanar a baya. Bitar da aka yi wa taken, TSARI DA SALON RUBUTUN SHIGA GASAR GAJEREN LABARI an yi ta ne domin taimakawa marubuta, musammam masu tasowa, dabarun rubuta gajerun labarai na shiga gasar labarai.
A kokarin da gidajen jaridu na Hausa da sauran kafafen labarai suke yi na ganin sun farfado da adabin Hausa, su kan shirya gasanni na rubuta labarai, kamar wadda a yanzu haka ake gudanarwa na Gasar Aminiya da ire-iren na su BBC Hausa da makamantansu. Domin taimakawa masu shiga irin wadannan gasanni, Bakandamiya ta shirya wannan bita kuma aka gabatar a taskarta ta yanar gizo, wato Bakandamiya.com a cikin zauren MARUBUTA wadda aka dauki tsawon kwanaki biyar ana yi duk rana daga karfe 8:00 pm zuwa 10:00 na dare.
Ga yadda bitar ta kasance kamar haka:
Rana ta farko
A rana ta farko, Malam ya gabatar da bitar ne da maudu’i mai matukar muhimmanci, wato maganar yawan adadin kalmomi da ake bukata a gajeren labari. Malam ya dora da cewa lallai idan marubuta ba su kula da sanin ka’idan rubutun Hausa ba, musamman hadewa da rabewar kalmomi, to ba za su cimma burinsu na cika ka’idojin gasa ba. Saboda a ko wacce gasa akwai adadin kalmomi kuma idan ba a san ka’idan rabewa da hadewa ba, ba za a iya tantance yawan kalmomi da su ke cikin labari ba.
Malam ya ba da misalai da dama na yadda rashin rabewa ko hadewar ke canza wa rubutu ma’ana yawa yawanci lokaci. A karshe ya baiwa mahalarta wannan bita dama kowa da kowa yin tambaya akan abinda aka tattauna, sannan daga bisani ya bi tambayoyin daya bayan daya ya amsa su. An rufe bitar wannan rana da baiwa mahalarta bitar aikin gida domin gwada abinda aka koyar da su.
Kuna iya karanta cikakken darasin da aka yin a wannan rana ta hanyar latsa nan.
Rana ta biyu
A wannan rana, Malam ya mai da hanakali ne akan ka’idoji da mai rubuta gajen labari ya kamata ya bi. Duk da cewa ya ce wadannan ka’idojin ba wai doka ba ne amma bin su na da muhimmanci. Ga ka’idojin kamar haka:
- Amfani da zababbun kalmomi
- Zaben waje da muhalli da lokaci
- Bai wa manufa muhimmanci
- Fayyace tauraro da irin burinsa
- Maida hankali kan jigo
- Takaitawa – Siffantawa, Yawan Taurari, Yawan
- Bayyana aikatau
Ya dauke su daya bayan daya ya yi bayani da bada misalai. Sannan daga karshe, mahalarta sun tattauna akan ko wani ka’ida kuma an ba su daman su ka yi tambayoyinsu kuma Malam ya amsa musu yadda ya kamata.
Ku karanta cikakken makala akan darasin rana ta biyu.
Rana ta uku
Rana ta uku kuma rana ce da Malam ya gabatar da matakan da ake bi wajen tsara labari, inda ya nuna wa mahalarta bitar cewa lallai-lallai domin labari ya inganta dole ne a tsara shi akan tubala masu kyau da inganci. Anan ne ya shigo da wani ma’auni ko in ce tubala da wani masani kuma kwararren marubuci mai suna, Michael Lengsfield, ya zo da su mai taken, Five Finger Pitch. Ya nuna wa mahalarta bitan da cewa duk labari ya na bukatan a tsara shi akan wadannan tubala domin samun ingantan shi. Ga Five Finger Pitch nan kamar haka:
- Genre
- Tauraro
- Goal
- Obstacles
- What is Important
Malam ya yi bayanin su daya bayan daya cikin tsanaki kuma ya nuna cikin misalai yadda ake tsara labari akan wadannan tubala. Malam ya rufe bitar wannan rana da bawa mahalarta aikin gida in da ya cewa kowa ya zo da tsarin labari akan tubalan Five Finger Pitch.
Za ku iya karanta cikakken darasin rana ta uku a wannan link.
Rana ta hudu
Game da matakan rubuta labari malam ya maida hankali a rana ta hudu. Ya nuwa cewa bayan an san matakan tsara labari to abu na gaba shi ne a san matakan da ake bi domin rubuta labari mai inganci da armashi. Duk da cewa ya nuna cewa wadannan matakai ba lallai ba ne to amma suna da muhimmanci saboda da yawa daga cikin masana ma suna bin wadannan matakai wajen rubuta labaransu. Ga matakan kamar yadda ya lissafo su:
- Tunani akan labarin da ake so a rubuta
- Tsara labari akan sikelin Five Finger Pitch
- Samar da ɗangogin labari watau Outline ko Index ko Flash card
- Gudanar da bincike
- Rubutu na farko
- Karantawa da yin gyare-gyare
- Mikawa masana ko abokai su duba labarin
- Sake yin gyara tare da tabbatar da sunayen taurari da wurare da kuma sarrafa kalmomi.
- Samar da taken da ya dace da labarin
Malam yace bin wandannan matakai suna da kyau amma ba dole sai an bi su duka ba. Samun dama ko rashin daman bin su wani lokacin ya danganta ne da irin lokaci da marabuci ya ke da shi a hannu.
Rana ta biyar
A rana ta biya wacce ita ce rana ta karshe na wannan bitar, Malam ya kawo misalan labarai ne daban-daban har guda biyar domin bawa mahalarta daman ganin abubuwan da aka koyar tsawon kwanakin bitar a aikace.
Kammalawa
A karshe, wannan bitar ta gudana cikin farinciki da annashuwa a yayinda mahalarta suka saki jiki sosai wajen bayar da gudumawarsu daga farko har karshen bitar. An samu mahalarta a kalla mutane 25 wadanda suka halarta kuma suka bada gudumawa, sannan Bakandamiya ta baiwa mutane 8 daga cikinsu, wadanda suka cika ka’ida shaida, wato certificate, kamar yadda ta yi alkawari. Lallai wannan bita ta yi nasara, kuma muna fatan wadanda suka halarta su yi amfani da ilimi da suka koya, amin.