Skip to content

Sabon tsari don kara ba wa marubuta damar samun kudi da labarinsu

Sabon tsari don kara ba wa marubuta damar samun kudi da labarinsu

Kai marubuci ne? Ke marubuciya ce?

Ko kun san Bakandamiya ta sabunta tsarikanta, ma’ana ta zo da sabon tsari inda marubuci zai iya sayar da labarinsa babi-babi, ya kuma cire kudinsa cikin sauki matukar ya cika sababbin ka’idojinta? Wannan ka’idoji ba masu wahala bane ba.

– Zaka shiga yarjejeniyar shekara daya ne da Bakandamiya, inda zaka wallafa littafin naka a manhajar Bakandamiya Hikaya na tsayin shekara daya kadai kafin ka sayar da shi a ko ina kake so.

– Littafin naka zai kasance sabo ne, baka taba saka shi a ko ina ba.

– Kalmomin kowane shafi kada ya gaza 2500.

Kuma kasan babu ruwanka da fargabar sai views ya cika? Abinda Bakandamiya take so dakai kawai shine:

– Ka tallata links din labarin a duk wani waje da kake saka litattafanka.

– Duk wanda yake so, ka tura shi Bakandamiya.

Bakandamiya zata biya ka daga 1k zuwa 3k duk babi, gwagwadon shaharar marubuci, yawan mutanen da suka yi subscribing domin littafin nashi.

Zaku iya tuntubar Bakandamiya kai tsaye ta:

Email: admin@bakandamiya.com

Phone: 09072304845

The Bakandamiya Team

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *