Alhamdulillahi cikin yardan Allah mai kowa mai komai an kammala zagaye na farko na gasar muhawarar da a yanzu haka ake gabatarwa a taskar Bakandamiya mai taken, Muhawarar Bakandamiya 2020. An kammala zagayen ne kuma a ranar 9/1/2021. Wannan zagayen shi ya fi duk zagaye-zagaye guda shida da mahawara ta kunsa tsayi da kuma yawan karawa da kungiyoyin marubuta za su ka yi.
Ga takaitaccen bayani game da wannan zagaye da kuma nasarori da aka samu.
Yawan rukunai da kuma karawa da aka yi
A wannan zagayen an fafata ne da kungiyoyi daban-daban da ke cikin rukunai guda takwas (8) da wannan gasa ta kunsa. Kowani rukuni akwai kungiyoyi guda hudu, kungiyoyi 32 ke nan duka, inda suka fatata a tsakaninsu a karawa har guda shidda; wato ko wacce kungiya ta samu daman karawa har sau uku ke nan a bangarenta a cikin rukuninta. Duk da cewa an samu wasu kungiyoyi kalilan da ba su halarci dukkanin karawarsu uku ba, to amma akasarin kungiyoyi sun halarta har zuwa kai karshen wannan zagaye.
Kungiyoyin da suka yi nasara
Kamar yadda aka tsara wannan muhawara, a karshen wannan zagaye wasu daga cikin kunyoyin za su ci gaba idan suka yi nasarar zuwa na daya (1st) ko na biyu (2nd), sannan wadanda suka zo na uku (3rd) da kuma na hudu (4th) za su bar gasar. An tantance nasarar kungiyoyi ne ta hanyar yawan maki da suka samu a rukuninsu.
Ga yadda abin ya kasance kamar haka:
1. Rukunin Bature Gagare
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st Haske Writers Association = Maki 218
2nd Potiskum Writers Association = Maki 210
2. Rukunin Balaraba Ramat Yakubu
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st Nguru Writers Association = Maki 215
2nd Zaman Amana Writers Association = Maki 213
3. Rukunin Dan Azumi Baba Cediyar ‘Yan Gurasa
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st Hazaka Writers Association = Maki 242
2nd Inside Arewa Wrters Association = 234
4. Rukunin Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st Nagarta Writers Association = Maki 250
2nd Proficient Writers Association = Maki 221
5. Rukunin Muhammad B. Zakari Kafin Hausa
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st Guild Writers of Nigeria = Maki 239
2nd Hakuri da Juriya Writers Association = Maki 237
6. Rukunin Dr. Bukar Usman, OON
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st Zamani Writers Association = Maki 235
2nd Gamzaki Writers Association = Maki 229
7. Rukunin Talatu Wada Ahmad
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st First Class Writers Association = Maki 240
2nd Karamci Writers Association = Maki 236
8. Rukunin Farfesa Yusuf Adamu
Kungiyoyin da suka yi nasara a wannan rukuni da kuma yawan makin da suka samu sun hada da;
1st Marubuta Kare Hakkin Al’umma = Maki 245
2nd Kainuwa Writers Association = Maki 237
Kammalawa
A karshe, kamar yadda ku ka gani a sama, kungiyoyi 16 ne su ka samu wucewa zuwa zagaye na biyu. Muna taya su murna matuka. Sannan a bangaren kungiyoyi 16 da basu samu daman wucewa ba kuma, muna yi musu fatan alkhairi da godiya bisa ba mu hadin kai da suka yi domin kaiwa wannan matakin. Insha Allah gasar muhawara za ta ci gaba kamar yadda aka tsara da zagaye na biyu a ranar 13/1/2021 mai zuwa.
Ma sha Allah Abu ya yi yadda ake so Allah ya bamu nasara baki daya
Amin Ya Rabb
Masha Allah ubangiji Allah ya bawa masu rabo sa’a ina muku fatan alkairi
Amin, madalla