Skip to content

Ka’idoji da jadawalin Muhawarar Bakandamiya 2020

Ka'idoji da Jadawalin Muhawara 2020

Ga kammalallen ka’idoji da jadawalin Muhawarar Bakandamiya na shekarar 2020.

ƘA’IDOJIN MUHAWARA

1. Za ayi wannan gasa ne a zauren Marubuta da ke manhajar Bakandamiya. Wajibi ne wanda duk za ayi wannan gasa da su, to su kasance a can www.bakandamiya.com

2. Kowacce ƙungiya zata bayar da wakilinta wanda zai gabatar da sunansa tare da sunan ƙungiyar da zai wakilta a ranar gabatar da muhawarar.

3. Ranar da za ayi Muhawarar za a bada topic wanda nan take wakilin ƙungiya zai ce ya ƙarɓa. To da zarar ya amsa cewa ya amsa lokacinsu zai fara kuma za a fitar da adadin lokacin da ake so kowa ya gama kawowa. A ƙasan posting da aka yi gabatarwa kowa anan zai zo ya amsa, sannan karku manta muhawara akace, dole komai a yi shi nan take ana bayar da lokaci kowa zai fara turo bayanai ko da guntu-guntu mutum ya kawo babu laifi. Kawai dai kar rubutun ya haura kalmomi ɗari shida (600) kuma kar yayi ƙasa da kalmomi ɗari biyar (500).

Idan kun yi ra’ayi  zaku iya kawowa da kalmomi ɗari-ɗari, da zarar kun yi typing kalma ɗari sai ku turo, sai ku yi hakan sau shida ko sau biyar. In kun gadama za ku iya rabawa biyu ko uku koma yanda kuka gadama, kuma zaku iya shiga wajen reply na abokin karawar ku bayar da amsa don kara samun hujja.

Daga ƙarshe alƙalai zasu tattara bayanan da kowa ya tura don yin maki.

4. Adadin kalmomin da ake buƙata ga duk wanda aka baiwa topic shi ne kada kalmomin su haura a ɗari shida (600) kuma kar su gaza a kalmomi ɗari biyar (500).

5. Alƙalai za su duba abubuwa kamar haka

a) Gabatarwa

b) Jigo

c) Balaga (isar da saƙo)

d) Hujja

e) Karin magana

f) Ƙa’idojin rubutu

g) Adadin kalmomi

h) Cikar lokaci

i) Yawan like (Daga 60 zuwa sama)

j) Yawan comments (Daga 20 zuwa sama)

k) Karkarewa

Wannan su za a duba wajen yin maki.

6. Za a rinka gabatar da karawar ƙungiyoyi a duk bayan kwana biyu,abin nufi yau in aka gabatar to za a tsallake kwana biyu a tsakani sannan a gabatar da wasu ƙungiyoyin.

7. Masu gabatar da Muhawarar ne kaɗai suke da ikon sanar da wani bayani daya danganci muhawarar don gudun kawo ruɗani.

8. Za ayi wannan muhawara ne a fili a idon kowa kuma lokaci ɗaya kowanne wakili zai zo ya ƙarɓi topic za a bada lokacin da kowacce za ta kawo bayanin data rubuto.

9. Za a rinƙa gabatar da wannan muhawara ne duk bayan kwanki biyu kuma da ƙarfe takwas na dare zuwa sha ɗaya dare, ƙungiyoyi huɗu ne za su rinƙa karawa a kowacce ranar da za a yi,haɗuwa biyu kenan a lokaci ɗaya.

10. Kamar yanda kuka gani a rubuce kowanne rukuni (group) akwai ƙungiyoyi guda huɗu wanda a cikin ƙungiya huɗun nan ana buƙatar ƙungiyoyi biyu ne za su tsallake su ne wadanda suka fi kowa yawan maki.

Karin bayani game da wannan tsarin group din:

Aƙalla kowace ƙungiya ɗaya sai ta fafata sau uku a kowane group ke nan. Misali:

> A vs B

> C vs D

> A vs C

> B vs D

> A vs D

> B vs C

Wannan iya rukuni (group ɗaya ke nan) watau fafatawa daban-daban sau 3, kowanne ɗaya zai fafata sau uku.

Sannan wurin fitar da na ɗaya da na biyu shi ma ana tara adadin makin kowane gabaɗaya, wanda ya fi kowa yawan maki a group shi ne na 1, sai mai bi masa a yawan maki. Watau 2 za su  tsallake zagaye na gaba, biyu za su fita.

Fatan an fahimci wannan bayanin, shin wancan (A vs D) da aka sanya misali ne A din kamar ace sunan wata kungiya ne,haka B din ko D din,ta haka kowa zai hadu da kowa a matakin group,in aka tsallaka gaba kuma ya zama siri daya kwale, akwai cikakken wannan bayani a jadawali sai a duba.

11. Ga maudu’ai da za ayi amfani da su lokacin muhawara domin kuyi bincike akansu. Karawa ta farko za a yi amfani da maudu’i na farko (K1), karawa ta biyu, maudu’i na biyu (K2), da haka har aje karawa ta karshe. To amma bangaren maudu’i da kungiya za ta yi magana akai shi sai lokacin karawa za a sani ta hanyar canki-canka. Kana a duba jadawalin karawar don ganin wani maudu’i ne zai dace da karawarku.

A kowane rana: Lokacin karawar farko zai fara ne 8:00 pm, Na biyu kuma 10:00 pm.

K1. Sayar da littafi ta internet da kuma sayarwa a kasuwa

K2. Wanne ne yafi…? Kasuwancin internet da kuma kasuwanci zama a shago.

K3. Wanne ne yafi amfani ga lafiyar dan adam sanyi ko zafi?

K4. Wa yake da laifi a matsalar fyaɗe gwamnati ko iyaye.

K5. Wa yake cin riba a hauhawar farashi, yan kasuwa ko gwamnati.

K6. Tsakanin karatu da aure wanne yafi muhimmanci ga ‘ya mace?

K7. Saurin isar da saƙo da kuma amfani ga mutane, Rubutu da waƙa.

K8. Tsakanin malamai da dalibai laifin waye wajen faduwa jarabawa?

K9. Lalacewar tarbiyyar ‘yan mata iyaye ko kawaye ne silar hakan?

K10.Tsakanin iska da ruwa wanne ne ya fi amfani ga ɗan adam?

K11.Soyayya kafin aure da soyayya bayan aure

K12. Kuɗi da sarauta

K13. Zuciya da Ƙwaƙwalwa

K14. Makarantar kwana da kuma je ka ka dawo.

K15. Kurumta da makanta, (rashin ido ko kunne)

K16. Me ke janyo lalacewar ‘ya’ya mata tsakanin talauci da jahilci?

K17. Tsakanin neman kuɗi da neman ilimi wanne yafi muhimmanci?

K18. Me ke janyo yawan mace-macen aure tsakanin rashin haƙuri da rashin tarbiya?

K19. Tsakanin tsaro da kiwon lafiya wanne yafi muhimmanci ga al’umma?

K20. Me ke janyo ta’addancin tsakanin jahilci da talauci da zalunci?

K21. Tsakanin mulkin soja da na farar hula wanne yafi dacewa ga ƙasar Nijeriya?

K22. Alhakin tarbiyar ‘ya’ya a wuyan wa ya rataya tsakanin uwa da uba?

K23. Tsakanin dabara da tunani wanne yafi wani?

K24. Me ke janyo satar amsa a jarrabawa tsakanin rashin fahimtar ɗalibai da kuma rashin koyarwar malamai yadda ya kamata?

K25. Me ke janyo cin hanci da rashawa tsakanin rashin gaskiya da rashin adalci?

K26. Tsakanin maganin gargajiya da na bature wanne yafi muhimmanci ga al’umma?

K27. Tsakanin lalacewar ‘ya mace da ɗa namiji wanne yafi muni a cikin al’umma?

K28. Tsakanin kasuwanci da aikin gwamnati wanne yafi?

K29. Tsakanin mafarauci da maharbi waye yafi jarumta?

K30. Noma da Kiwo. Wanne ne yafi muhimmanci a rayuwar dan adam?

K31. Bayan mutuwar uba, wanne yafi dacewa da rikon yaransa, kaka ta wurin uwa ko kaka ta wurin uba?

K32. Wanne yafi muhimmanci a soyayya, kudi ko kulawa?

K33. Wa ya fi taimakawa wajen gyara tarbiyyar yara malamai ko iyaye?

K34. Tsakanin kyawawan halaye da ilimi wane yafi amfani ga dan Adam?

K35. Wane ya fi saurin illata zuciya tsakanin tsananin so da tsananin kishi?

K36. Da ka rayu da wanda kake so da ka rayu da wanda yake sonka wane ya fi dadi?

K37. Tsakanin mai macce ɗaya da mai macce biyu wane yafi samun kulawa da kwanciyar hankali?

K38. Auren Hadi da Auren soyayya wane yafi?

K39. Da auren mai kudi mai mata da auren talaka mara mata, wanne ya fi?

K40. Auren saurayi mara kwabo da auren dattijo mai abin hanu, wane ya fi?

K41. Da arziki ga danka da arziki ga diyarka, wane ya fi?

K42. Auren ɗan kasuwa da auren ma’aikaci wanne ya fi?

K43. Laifin waye ke jawo macen aure bin wasu mazan a waje, laifin mijin ne ko na matar?

K44. Shin ya kamata a ba mace shugabanci ko kuwa bai kamata ba?

K45. Yawaitar fyade laifin gwamnati ne ko kuma al’umma? (Al’umma ta kunshi iyaye, matasa da sauran mutane).

K46. Kaifin basirar yaro da fahimtar karatu yana samo tushe ne daga kulawar iyayensa ko kuwa kulawar malamai ne?

K47. Dangin miji da dangin mata, wanne yafi kawo matsala?

K48. Noman rani da noman damina, wanne yafi riba ga manoma?

K49. Wane ne ya fi matsala da hatsari a tsakanin direba mai waige-waige da direba mai barci?

K50. Miji mai duka da miji mai horo da yunwa, wanne ne yafi illa?

K51. Rashin hannu da rashin kafa wanne ne yafi zama tawaya ga dan adam?

K52. Yawan hatsari da ake yi laifin gwannati ne ko na direbobi?

K53. Matsalar cin hanci laifin gwannati ne ko na masu bayar da cin hancin?

K54. Karatu a cikin kasar mutum ya fi karatu a kasar waje?

K55. Karanta fasaha (arts) ya fi haifar da ingantaccen dalibi ga kasa akan karanta kimiyya (science)

K56. Wani abinci ya fi muhimmanci tsakanin madara da zuma?

K57. Noman kayan gona na sayarwa ya fi muhimmanci ga kasa akan noman kayan abinci.

K58. Talabijin da rediyo, wanne ya fi amfani ga gwamnati wajen isar da sako?

K59. Auren zumunci (dan’uwa ko yar’uwa) ya fi auren bare.

K60. Kagaggun labarai fun fi isar da sako akan labarai na gaskiya.

K61. Wanne ya fi saurin tasirin canja mutum tsakanin karanta littafi da kallon film?

K62. Mulkin gargajiya ya fi mulkin siyasa kawo ci gaba a kasa.

K63. Tsakanin rukunin samari maza da yanmata wa ya fi yaudara?

K64. Wanne ne yafi sauƙi da kuma samun ilimi sosai, karatu ta internet ko kuma karatu na zama a aji?

JADAWALIN MUHAWARA

ZAGAYE NA DAYA

RUKUNIN BATURE GAGARE

(Ranar Nazir Adam Salih)

K1. (24/11/2020): Potiskum Writers Association vs Taurari Writers Association

K2. (24/11/2020): Dutse Writers Association vs Haske Writers Assocation

(Ranar Fauziyya D. Sulaiman)

K17. (10/12/2020): Haske Writers Association vs Taurari Writers Association

K18. (10/12/2020): Dutse Writers Association vs Potiskum Writers Association

(Ranar Alkamis B. Makwarari)

K33. (26/12/2020): Haske Writers Association vs Potiskum Writers Association

K34. (26/12/2020): Taurari Writers Association vs Dutse Writers Association

RUKUNIN BALARABA RAMAT YAKUBU

(Ranar Zulaihat Sani Kagara)

K3. 26/11/2020: Nguru Writers Association vs Zaman Amana Writers Association

K4. 26/11/2020: Rumbilhak Writers Association vs Strong Pen Writers Association

(Ranar Rahama Abdul Majid)

K19. (12/12/2020): Zaman Amana Writers vs Rumbilhak Writers Association

K20. (12/12/2020): Strong Pen Writers Association vs Nguru Writers Association

(Ranar Aminu Ladan Abubakar Ala)

K35. (28/12/2020): Zaman Amana vs Strong Pen Writers Association

K36. (28/12/2020): Rumbilhak Writers Association vs Nguru Writers Association

RUKUNIN DAN AZUMI BABA CEDIYAR ‘YAN GURASA

(Ranar Tanko Mani)

K5. (28/11/2020): Hazaka Writers Association vs Yobe Authors Forum

K6. (28/11/2020): Mizani Writers Association vs Inside Arewa Writers Association

(Ranar Ahmad Muhd Zaharaddeen)

K21. (14/12/2020): Mizani Writers Association vs Hazaka Writers Association

K22. (14/12/2020): Yobe Authors Forum v Inside Arewa Writers Association

(Ranar Bashir Ahmad)

K37. (30/12/2020): Inside Arewa Writers Association vs Hazaka Writers Association

K38. (30/12/2020): Yobe Authors Forum vs Mizani Writers Association

RUKUNIN ADO AHMAD GIDAN DABINO, MON

(Ranar Hadi Abdullahi Alkalanci)

K7. (30/11/2020): Proficient Writers Association vs Yobe Writers Association

K8. (30/11/2020): Nagarta Writers Association vs Al’umma Writers Association

(Ranar Bashir Sanda Gusau)

K23. (16/12/2020): Al’umma Writers Association vs Yobe Writers Associaton

K24. (16/12/2020): Nagarta Writers Association vs Proficient Writers Association

(Ranar Jamila Adamu yaro)

K39. (1/1/2021): Al’umma Writers Assocition Vs Profient Writers Association

K40. (1/1/2021): Yobe Writers Association Vs Nagarta Writers Association

RUKUNIN MUHAMMAD B. ZAKARI KAFIN HAUSA

(Ranar Nafisa Muhammad Lawan)

K9. (2/12/2020): Ana Tare Writers Association Vs Writers Guild of Nigeria

K10. (2/12/2020): Gaskiya Writers Association Vs Hakuri da Juriya Writers Association

(Ranar Habibu Hudu Darazo)

K25. (18/12/2020): Writers Guild of Nigeria Vs Gaskiya Writers Association

K26. (18/12/2020): Hakuri Da Juriya Writers Association Vs Ana Tare Writers Association

(Ranar Abdullahi Mukhtar Yaron Malam)

K41. (3/1/2021): Gaskiya Writers Association Vs Ana Tare Writers Association

K42. (3/1/2021): Writers Guild of Nigeria Vs  Hakuri Da Juriya Writers Association

RUKUNIN DR. BUKAR USMAN

(Ranar Bashar Farouq Roukba)

K11. (4/12/2020): Arewa Writers Association Vs Golden Pen Writers Association

K12. (4/12/2020): Zamani Writers Association Vs Gamzaki Writers Association

(Ranar Dr. Bilkisu Yuseef Ali)

K27. (20/12/2020): Golden Pen Writers Association Vs Gamzaki Writers Association

K28. (20/12/2020): Zamani Writers Association Vs Arewa Writers Association

(Ranar Prof. Sa’idu Muhammad Gusau)

K43. (5/1/2021): Golden Pen Writers Association Vs Zamani Writers Association

K44. (5/1/2021): Arewa Writers Association Vs Gamzaki Writers Association

RUKUNIN TALATU WADA AHMAD

(Ranar Dr. Hasiya Malam Nafi’u)

K13. (6/12/2020): First Class Writers Association Vs Zazzau Emirate Writers Association

K14. (6/12/2020): Pen Writers Association Vs Karamci Wirter Association

(Ranar Bilkisu Funtua)

K29. (22/12/2020): Karamci Writers Association Vs First Class Writers Association

K30. (22/12/2020): Zazzau Emirates Writers Association Vs Pen Writers Association

(Ranar Abubakar Gimba)

K45. (7/1/2021): Pen Writers Association Vs First Class Writers Association

K46. (7/1/2021): Zazzau Emirates Writers Association Vs Karamci Writers Association

RUKUNIN PROF. YUSUF ADAMU

(Ranar Zaharaddin Ibrahim Kalla)

K15. (8/12/2020): Kainuwa Writers Association Vs Hikima Writers Association

K16. (8/12/2020): Intelligent Writers Association Vs Marubuta Kare Hakkin Al’umma

(Ranar Ahmad Ingawa)

K31. (24/12/2020): Hikima Writers Association Vs Intelligent Writers Association

K32. (24/12/2020): Kainuwa Writers Association Vs Marubuta Kare Hakkin Al’umma

(Ranar Umaru Dembo)

K47. (9/1/2021): Intelligent Writers Association Vs Kainuwa Writers Association

K48. (9/1/2021): Hikima Writers Association Vs Marubuta Kare Hakkin Al’umma

ZAGAYE NA BIYU

(Ranar Bala Anas Babinlata)

K49. (13/1/2021): Na 1 a RUKUNIN BATURE GAGARE da na 2 a RUKUNIN BALARABA RAMAT YAKUBU

K50. (13/1/2021): Na 2 a RUKUNIN BATURE GAGARE da na 1 a RUKUNIN BALARAB RAMAT YAKUBU

(Ranar Badamasi Shu’aibu Burji)

K51. (15/1/2021): Na 1 a RUKUNIN DAN AZUMI BABA CEDIYAR ‘YAN GURASA da na 2 a RUKUNIN ADO AHMAD GIDAN DABINO, MON

K52. (15/1/2021): Na 2 a RUKUNIN DAN AZUMI BABA CEDIYAR ‘YAN GURASA da na 1 a RUKUNIN ADO AHMAD GIDAN DABINO, MON

(Ranar Aminu Abdu Na’inna)

K53. (17/1/2021): Na 1 a RUKUNIN MUHAMMAD B. ZAKARI KAFIN HAUSA da na 2 a RUKUNIN DR. BUKAR USMAN

K54. (17/1/2021): Na 2 a RUKUNIN MUHAMMAD B. ZAKARI KAFIN HAUSA da na 1 a RUKUNIN DR. BUKAR USMAN

(Ranar Magaji Danbatta)

K55. (19/1/2021): Na 1 a RUKUNIN TALATU WADA AHMAD da na 2 a RUKUNIN PROF. YUSUF ADAMU

K56. (19/1/2021): Na 2 a RUKUNIN TALATU WADA AHMAD da na 1 a RUKUNIN PROF. YUSUF ADAMU

ZAGAYE NA UKU (QUARTER FINAL)

(Ranar Hamma Danjuma Kasagi)

K57. (23/1/2021): Fafatawar kusa da na kusa da na karshe (Kungiyoyi biyu da suka yi nasara a Ranar Anas Babibinlata)

K58. (23/1/2021): Fafatawar kusa da na kusa da na karshe (Kungiyoyi biyu da suka yi nasara a Ranar Badamasi Shu’aibu Burji)

(Ranar Farfesa Abdulkadir Dangambo)

K59. (25/1/2021) Fafatawar kusa da na kusa da na karshe (Kungiyoyi biyu da suka yi nasara a Ranar Aminu Abdu Na’inna)

K60. (25/1/2021) Fafatawar kusa da na kusa da na karshe (Kungiyoyi biyu da suka yi nasara a Ranar Magaji Danbatta)

ZAGAYE NA HUDU (SEMI-FINAL)

(Ranar Farfesa Ibarahim Yaro Yahaya)

K61. (29/1/2021): Fafatawar kusa da na karshe (Kungiyoyi biyu da suka yi nasara a Ranar Hamma Danjuma Kasagi)

K62. (29/1/2021): Fafatawar kusa da na karshe (Kungiyoyi biyu da suka yi nasara a Ranar Farfesa Abdulkadir Dangambo)

ZAGAYE NA BIYAR (NEMAN NA UKU)

(Ranar Hafsat Abubukar Sa’id)

K63. (2/2/2021): Fafatawar neman na uku (Kungiyoyi biyu da ba su samu nasara ba a Ranar Farfesa Ibrahim Yaro Yahara)

ZAGAYE NA KARSHE (FINAL)

(Ranar Dr. Abubakar Imam)

K64. (6/2/2021): Fafatawar karshe (Kungiyoyi biyu da suka yi nasara a Ranar Farfesa Ibrahim Yaro Yahara)

Duk ranakun da za a kara a wannan muhawara za a fara ne da karfe 8:00 pm. Kuma kamar yadda muka ambata a farko, za a gudanar da wannan muhawara ne a nan ZAUREN MARUBUTA dake taskar BAKANDAMIYA zai gudana. Sai ku sauke manhajar Bakandamiya sannan kuma ku yi rajista don samun damar halarta.

Don neman ƙarin bayani sai a tuntubi:

07033704523

08037442582

08144410022

Bayani:

K1 = Na nufin KARAWA TA 1; K2 = Na nufin KAWARA TA 3; har zuwa karawa ta karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *