Ga ka’idojin Muhawarar Bakandamiya 2020 kamar haka:
1. Za ayi wannan gasa ne a zauren Marubuta da ke manhajar Bakandamiya. Wajibi ne wanda duk za ayi wannan gasa da su, to su kasance a can www.bakandamiya.com
2. Kowacce ƙungiya zata bayar da wakilinta wanda zai gabatar da sunansa tare da sunan ƙungiyar da zai wakilta a ranar gabatar da muhawarar.
3. Ranar da za ayi Muhawarar za a bada topic wanda nan take wakilin ƙungiya zai ce ya ƙarɓa. To da zarar ya amsa cewa ya amsa lokacinsu zai fara kuma za a fitar da adadin lokacin da ake so kowa ya gama kawowa. A ƙasan posting da aka yi gabatarwa kowa anan zai zo ya amsa, sannan karku manta muhawara akace, dole komai a yi shi nan take ana bayar da lokaci kowa zai fara turo bayanai ko da guntu-guntu mutum ya kawo babu laifi. Kawai dai kar rubutun ya haura kalmomi ɗari shida (600) kuma kar yayi ƙasa da kalmomi ɗari biyar (500).
Idan kun yi ra’ayi zaku iya kawowa da kalmomi ɗari-ɗari, da zarar kun yi typing kalma ɗari sai ku turo, sai ku yi hakan sau shida ko sau biyar. In kun gadama za ku iya rabawa biyu ko uku koma yanda kuka gadama, kuma zaku iya shiga wajen reply na abokin karawar ku bayar da amsa don kara samun hujja.
Daga ƙarshe alƙalai zasu tattara bayanan da kowa ya tura don yin maki.
4. Adadin kalmomin da ake buƙata ga duk wanda aka baiwa topic shi ne kada kalmomin su haura a ɗari shida (600) kuma kar su gaza a kalmomi ɗari biyar (500).
5. Alƙalai za su duba abubuwa kamar haka
a) Gabatarwa
b) Jigo
c) Balaga (isar da saƙo)
d) Hujja
e) Karin magana
f) Ƙa’idojin rubutu
g) Adadin kalmomi
h) Cikar lokaci
i) Yawan like (Daga 60 zuwa sama)
j) Yawan comments (Daga 20 zuwa sama)
k) Karkarewa
Wannan su za a duba wajen yin maki.
6. Za a rinka gabatar da karawar ƙungiyoyi a duk bayan kwana biyu,abin nufi yau in aka gabatar to za a tsallake kwana biyu a tsakani sannan a gabatar da wasu ƙungiyoyin.
7. Masu gabatar da Muhawarar ne kaɗai suke da ikon sanar da wani bayani daya danganci muhawarar don gudun kawo ruɗani.
8. Za ayi wannan muhawara ne a fili a idon kowa kuma lokaci ɗaya kowanne wakili zai zo ya ƙarɓi topic za a bada lokacin da kowacce za ta kawo bayanin data rubuto.
9. Za a rinƙa gabatar da wannan muhawara ne duk bayan kwanki biyu kuma da ƙarfe takwas na dare zuwa sha ɗaya dare, ƙungiyoyi huɗu ne za su rinƙa karawa a kowacce ranar da za a yi,haɗuwa biyu kenan a lokaci ɗaya.
10. Kamar yanda kuka gani a rubuce kowanne rukuni (group) akwai ƙungiyoyi guda huɗu wanda a cikin ƙungiya huɗun nan ana buƙatar ƙungiyoyi biyu ne za su tsallake su ne wadanda suka fi kowa yawan maki.
Karin bayani game da wannan tsarin group din:
Aƙalla kowace ƙungiya ɗaya sai ta fafata sau uku a kowane group ke nan. Misali:
> A vs B
> C vs D
> A vs C
> B vs D
> A vs D
> B vs C
Wannan iya rukuni (group ɗaya ke nan) watau fafatawa daban-daban sau 3, kowanne ɗaya zai fafata sau uku.
Sannan wurin fitar da na ɗaya da na biyu shi ma ana tara adadin makin kowane gabaɗaya, wanda ya fi kowa yawan maki a group shi ne na 1, sai mai bi masa a yawan maki. Watau 2 za su tsallake zagaye na gaba, biyu za su fita.
Fatan an fahimci wannan bayanin, shin wancan (A vs D) da aka sanya misali ne A din kamar ace sunan wata kungiya ne,haka B din ko D din,ta haka kowa zai hadu da kowa a matakin group,in aka tsallaka gaba kuma ya zama siri daya kwale, akwai cikakken wannan bayani a jadawali sai a duba.
11. Ga maudu’ai da za ayi amfani da su lokacin muhawara domin kuyi bincike akansu. Karawa ta farko za a yi amfani da maudu’i na farko (K1), karawa ta biyu, maudu’i na biyu (K2), da haka har aje karawa ta karshe. To amma bangaren maudu’i da kungiya za ta yi magana akai shi sai lokacin karawa za a sani ta hanyar canki-canka. Kana a duba jadawalin karawar don ganin wani maudu’i ne zai dace da karawarku.
A kowane rana: Lokacin karawar farko zai fara ne 8:00 pm, Na biyu kuma 10:00 pm.
K1. Sayar da littafi ta internet da kuma sayarwa a kasuwa
K2. Wanne ne yafi…? Kasuwancin internet da kuma kasuwanci zama a shago.
K3. Wanne ne yafi amfani ga lafiyar dan adam sanyi ko zafi?
K4. Wa yake da laifi a matsalar fyaɗe gwamnati ko iyaye.
K5. Wa yake cin riba a hauhawar farashi, yan kasuwa ko gwamnati.
K6. Tsakanin karatu da aure wanne yafi muhimmanci ga ‘ya mace?
K7. Saurin isar da saƙo da kuma amfani ga mutane, Rubutu da waƙa.
K8. Tsakanin malamai da dalibai laifin waye wajen faduwa jarabawa?
K9. Lalacewar tarbiyyar ‘yan mata iyaye ko kawaye ne silar hakan?
K10.Tsakanin iska da ruwa wanne ne ya fi amfani ga ɗan adam?
K11.Soyayya kafin aure da soyayya bayan aure
K12. Kuɗi da sarauta
K13. Zuciya da Ƙwaƙwalwa
K14. Makarantar kwana da kuma je ka ka dawo.
K15. Kurumta da makanta, (rashin ido ko kunne)
K16. Me ke janyo lalacewar ‘ya’ya mata tsakanin talauci da jahilci?
K17. Tsakanin neman kuɗi da neman ilimi wanne yafi muhimmanci?
K18. Me ke janyo yawan mace-macen aure tsakanin rashin haƙuri da rashin tarbiya?
K19. Tsakanin tsaro da kiwon lafiya wanne yafi muhimmanci ga al’umma?
K20. Me ke janyo ta’addancin tsakanin jahilci da talauci da zalunci?
K21. Tsakanin mulkin soja da na farar hula wanne yafi dacewa ga ƙasar Nijeriya?
K22. Alhakin tarbiyar ‘ya’ya a wuyan wa ya rataya tsakanin uwa da uba?
K23. Tsakanin dabara da tunani wanne yafi wani?
K24. Me ke janyo satar amsa a jarrabawa tsakanin rashin fahimtar ɗalibai da kuma rashin koyarwar malamai yadda ya kamata?
K25. Me ke janyo cin hanci da rashawa tsakanin rashin gaskiya da rashin adalci?
K26. Tsakanin maganin gargajiya da na bature wanne yafi muhimmanci ga al’umma?
K27. Tsakanin lalacewar ‘ya mace da ɗa namiji wanne yafi muni a cikin al’umma?
K28. Tsakanin kasuwanci da aikin gwamnati wanne yafi?
K29. Tsakanin mafarauci da maharbi waye yafi jarumta?
K30. Noma da Kiwo. Wanne ne yafi muhimmanci a rayuwar dan adam?
K31. Bayan mutuwar uba, wanne yafi dacewa da rikon yaransa, kaka ta wurin uwa ko kaka ta wurin uba?
K32. Wanne yafi muhimmanci a soyayya, kudi ko kulawa?
K33. Wa ya fi taimakawa wajen gyara tarbiyyar yara malamai ko iyaye?
K34. Tsakanin kyawawan halaye da ilimi wane yafi amfani ga dan Adam?
K35. Wane ya fi saurin illata zuciya tsakanin tsananin so da tsananin kishi?
K36. Da ka rayu da wanda kake so da ka rayu da wanda yake sonka wane ya fi dadi?
K37. Tsakanin mai macce ɗaya da mai macce biyu wane yafi samun kulawa da kwanciyar hankali?
K38. Auren Hadi da Auren soyayya wane yafi?
K39. Da auren mai kudi mai mata da auren talaka mara mata, wanne ya fi?
K40. Auren saurayi mara kwabo da auren dattijo mai abin hanu, wane ya fi?
K41. Da arziki ga danka da arziki ga diyarka, wane ya fi?
K42. Auren ɗan kasuwa da auren ma’aikaci wanne ya fi?
K43. Laifin waye ke jawo macen aure bin wasu mazan a waje, laifin mijin ne ko na matar?
K44. Shin ya kamata a ba mace shugabanci ko kuwa bai kamata ba?
K45. Yawaitar fyade laifin gwamnati ne ko kuma al’umma? (Al’umma ta kunshi iyaye, matasa da sauran mutane).
K46. Kaifin basirar yaro da fahimtar karatu yana samo tushe ne daga kulawar iyayensa ko kuwa kulawar malamai
A latsa nan don ganin cikakken jadawalin muhawarar.